Ikirarin nasara a yakin Gaza
August 28, 2014Talla
Shugabannin Isra'ila da na Falasdinawa ko wannensu na yin ikirarin samun nasara a yakin da suka gwabza sama da wata guda, bayan tsagaita wuta a shekaran jiya Talata. Firaministan Isra'ila Benjamin Netenyahu ya yi gargadin cewa bazai lamunta da duk wani harin roka da zai fito a bangaren Falasdinawa, inda ma yace zai maida martani mai muni. Ana su bangaren shugabannin Hamas a Gaza sun yi ikirarin tilastawa Isra'ila ta janye. A halinda ake ciki mazauna birnin Gaza sun fara fitowa a bainal jama'a, inda wadanda ke da sauran gidajensu da ba'a rusa ba, suke komawa gidajensu. Wadanda aka ruguzawa gidajensu kuwa na ta yawo kan titi.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu