Ikirari kan cin zabe a kasar Tunisiya
December 22, 2014Talla
Da yake magana 'yan mintoci kadan bayan rufe runfunan zabe, Mohsen Marzouk daraktan yakin neman zaben Baji Elsibsi cewa ya yi bisa dukkan alamun da suke gani da kuma sakamakon da ke hannunsu, na nuni da cewa dan takararsu ne ya yi nasara a zaben. Tuni dai ya yi wani jawabi a gaban dumbun magoya bayansa, don nuna godiyarsa a garesu ganin yadda suka fito suka yi zabe. Sai dai daga nashi bangare Shugaba mai barin gado Moncef Marzouki, ya nuna adawarsa ga wannan ikirari, inda ya zargi bangaren na Elsibsi da taka ka'idojin demokradiyya ta hanyar ayyana kansa kafin sakamakon hukumar zabe.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Mohammad Nasiru Awal