Idrissa na neman gaskiya kan kudin makaman Nijar | NRS-Import | DW | 09.12.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

NRS-Import

Idrissa na neman gaskiya kan kudin makaman Nijar

Wasu kungiyoyin farar hula a Nijar sun shigar da kara a gaban kotu domin ta bi kadin almundahana da dukiyar kasar da aka yi a ma'aikatar tsaro da ya kai fiye da Euro miliyan 115 tsakanin shekara ta 2017 zuwa 2019.

Kakakin rukunin kungiyoyin Nijar da suka shigar da kara Ali Idrissa ya ce suna bukatar kotu da ta kaddamar da bincike domin gano duk wasu wadanda suke da hannu wajen barnata dukiyar al'umma komai matsayinsa, tare da hukunta shi a gaban doka.

Ba tun yau ba ne ake ta tayar da jijiyoyyin wuya game da batun na karkata dukiyar da gwamnatin kasar ke warewa wajen tabbatar da tsaro, lamarin da ya haifar da zanga-zanga a cikin watan Maris na wannan shekara, biyo bayan wani kazamin harin da ya halaka sojan Nijar akalla 200 a wasu jerin hare-haren 'yan ta'adda a yammacin kasar.

Fiye da Euro miliyan 115 ne suka salwanta tsakanin shekara ta 2017 zuwa 2019 a ma'aikatar tsaron Jamhuriyar Nijar.