Idris Deby dan siyasa ne na kasar Chadi wanda ya hau kan kujerar shugaban kasa a shekarar 1990 bayan da aka kawo karshen mulkin Hissne Habre.
An dai haifi Deby a shekarar 1952 kuma yanzu haka ya na daga cikin shugabannin nahiyar Afirka da suka jima suna rike da madafun iko.