1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

ICG: Babu alamun Boko Haram ta fara saduda

July 7, 2020

Kungiyar International Crisis Group mai sanya ido a kan rigingimun da ke faruwa a duniya ta sanar cewa rundunar tsaron yankin tafkin Chadi mai suna MNJTF ta gaza cimma muradunta na yaki da Boko Haram.

https://p.dw.com/p/3etPB
Abubakar Shekau
Hoto: picture alliance/AP Photo

A cikin wani sabon rahoto da kungiyar International Crisis Group ta fitar a wannan Talata ta ce mayakan jihadi sun yi nasarar sake farfadowa a sakamakon yadda kasashen yankin suka gaza samar wa rundunar tsaron MNJTF din kudi da kayan aiki. Kungiyar ta ce a bisa binciken da ta gudanar babu wata alama da ke nuna cewa mayakan Boko Haram sun fara saduda.

Tun a shekara ta 2014 ne dai kasashen Kamaru da  Chadi da Nijar gami da Najeriya suka suka kafa wannan runduna domin magance hare-haren Boko Haram, sai dai acewar International Crisis Group gwamnatocin wadannan kasashen na bukatar yi wa rundunar garambawul ta hanyar gyara tsarin tattara bayanan sirri da magance cin zarafin mutane da ake zargin rundunar da shi.