ICC: Soma shari′ar rosa kaburburan waliyai a Mali | Labarai | DW | 30.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

ICC: Soma shari'ar rosa kaburburan waliyai a Mali

A wannan Laraba ce Ahmad Al-Faqi Al-Mahdi jagoran wata kungiyar masu kaifin kishin Islama ta kasar Mali ke fiskantar shari'a bisa umarnin rusa wuraren tarihi a Tombouctou

Jagoran kungiyar masu kaifin kishin Islama ta kasar Mali da ke da alaka da kungiyar Al-kaida, zai bayyana a gaban kotun hukunta manyan laifukan yaki ta duniya wato ICC. Kotun na zargin mutuman mai suna Ahmad Al-Faqi Al-Mahdi da bada umarnin rusa kaburburan waliyai na tarihi a shekara ta 2012.

Wannan dai shi ne karo na farko da kotun ta ICC za ta gudanar da shari'a kan batun rusa wasu wuraren tarihi na addini. A karshen makon da ya gabata ne dai aka kawo Ahmad Al-Faki Al-Mahdi wanda ke tsare a kasar Nijar zuwa gidan kurkukun kotun ta ICC da ke a birnin Hague.