Hunkunci a kan ′yan Taliban waɗanda suka nemi kashe Malala Yousafzai | Labarai | DW | 30.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hunkunci a kan 'yan Taliban waɗanda suka nemi kashe Malala Yousafzai

Wata kotu a Pakistan ta yanke hukuncin ɗaurin rai da rai ga wasu mutane guda goma wanda suka harbi Malala.

Kotun wacce ke yaƙi da ta'addanci ta samu mutanen da laifin yunƙurin hallaka Malala a shekaru 2012 a lokacin tana da shekaru 15.

A harin da suka kai mata a kan hanyarta ta zuwa makaranta a maifarta a garin Mingora da ke a yankin arewa maso yammacin Pakistan inda suka harbeta a ka.Harin wanda Ƙungiyar Taliban ta yi iƙirarin kai wa a cikin wata wasiƙa da ta aike wa Malala ta ce ta yi haka ne a kan fafutukar da take na samar da ilimin boko ga yara a Pakistan.