1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hungary za ta fice daga kotun ICC

Zainab Mohammed Abubakar
April 3, 2025

Framinista Orban ya ayyana ficewar kasar daga kotun ta kasa da kasa a yayin ziyarar takwaransa na Isra'ila a Benjamin Netanyahu a Budapest.

https://p.dw.com/p/4segb
Hoto: Attila KISBENEDEK/AFP

Kasar Hungary ta ce za ta fice daga kotun hukunta manyan laifukan yaki ta duniya, a daidai lokacin da Firaminista Viktor Orban ya karbi bakuncin takwaransa na Isra'ila Benjamin Netanyahu, wanda kotun ta zarge shi da aikata laifukan yaki a Gaza.

Sanarwar da gwamnati ta bayar na fara shirin janyewar na tsawon shekara, ya zo ne a daidai lokacin da Orban ya tarbi Netanyahu a Budapest babban birnin kasar a ziyararsa ta farko zuwa Turai tun 2023.

An gayyaci Netanyahu a watan Nuwamban da ya gabata, kwana guda bayan da kotun ICC ta bayar da sammacin kama shugaban na Isra'ila kan laifukan cin zarafin bil'adama da laifukan yaki.

Orban, wanda ya yi alkawarin ba zai zartar da sammacin ba, ya karbi Netanyahu da faretin girmamawa ta soja.