1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hungary: Orban ya lashe zabe a karo na uku

Ramatu Garba Baba
April 9, 2018

Jam’iyyar Fidesz ta Firaiminista Viktor Orban ta lashe akasarin kujerun 'yan majalisa a zaben da ya gudana a ranar Lahadin da ta gabata, jam’iyyar ta samu kashi 48.8 cikin dari na kuri’un da aka kada.

https://p.dw.com/p/2vhHG
Ungarn Wahlen Viktor Orban Wahlsieg Jubel
Hoto: Reuters/L. Foeger

Da wannan sakamako, Firaministan zai ci gaba da jan ragamar mulki a karo na uku, ya kuma bayyana farin cikinsa inda ya ke cewa zaben ya kasance mai matukar muhimmanci ga makomar kasar ta Hungary, sakamakon ya nuna yadda jam'iyyar ta yi nasarar lashe kujeru akalla dari da talatin da uku daga cikin dari da casa'in da tara.

Alkaluma sun yi nuni da cewa an sami fitowar jama'a fiye da yadda lamarin ya kasance a babban zaben kasar da aka yi shekaru hudu da suka gabata. Kasashen Turai da ke da tsamin dangantaka da Orban bisa kafewar da ya yi kan rashin amincewa da tsarin kungiyar EU na rarraba ‘yan gudun hijira a tsakanin kasashe mambobin kungiyar sun mayar da martani kan zaben kasar.