Human Rights Watch ta zargi Shell da Najeriya | Labarai | DW | 04.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Human Rights Watch ta zargi Shell da Najeriya

Ƙungiyar ta zargesu da rashin kulawa wajen share ɗanya man fetur ɗin da ya tsiyaya a Ogoni da ke a Naija Delta wanda ya gurɓata muhali.

Wani sabon rahoto da Ƙungiyar kare hakin bil addama ta Human Rights Watch ta bayyana ya zargi kamfanin mai na Shell da hukumonin Najeriya. Da gaza taɓuka wani abu, wajen kauwar da tsiyayar ɗayan man fetur wanda ya guɓarta muhali a Ogoni da ke a Naija Delta da ke a yankin kudancin ƙasar.

A cikin wata sanarwa da ta bayyana shugabar wata ƙungiyar da ke fafutukar kare muhali. Gowin Ojo wacce ƙungiyarta ta Friends of The Earth ke tare da ƙungiyar ta Human Rights Wacht, ta ce rashin share ɗayan man da ya kwararra a yankin na Ogoni, ya janyo cikas ga manoma da musunta wajen gudanar da harkokinsu.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe