Hukuncin shekaru 35 ga mutumin da ya ba wa Wikileaks bayanai | Labarai | DW | 21.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukuncin shekaru 35 ga mutumin da ya ba wa Wikileaks bayanai

Bradkey Manning wanda sojan Amirka ne mai shekaru 25, ya ba wa shafin intanet na Wikileaks dubban bayanan asirin sojan Amirka da na diplomasiyya.

An yanke wa Bradley Manning da ya tsegunta wa shafin Wikileaks labaran asirin Amirka hukuncin daurin shekaru 35 a kurkuku. Wata mai shari'a a kotun soji dake Fort Meade kusa da birnin Washington ta ba da wannan sanarwa. Bradkey Manning wanda sojan Amirka ne mai shekaru 25, ya ba wa Wikileaks dubban bayanan asirin sojan Amirka da na diplomasiyya. A karshen watan Yuli aka same shi da laifin tona asirin kasa, leken asiri da satar bayanai ta komfuta da kuma yi wa kasa sata. Sai dai an wanke shi daga zargi mafi tsauri wato taimaka wa abokan gaba. Masu shigar da kara sun nemi kotu ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 60 a kurkuku.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe