Hukuncin kisan ′yan Ostareliya a Indonesiya | Labarai | DW | 24.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukuncin kisan 'yan Ostareliya a Indonesiya

Shugaba Widodo na kasar ta Indonesiya ya bayyana cewa babu gudu ba ja da baya a dangane da hukuncin kisan da aka tsara a wannan mako.

Joko Widodo

Joko Widodo: Shugaban kasar Indonesiya

Wani alkalin kotu a kasar Indonesiya ya yi fatali da bukatar daukaka kara da aka gabatar masa sakamakon wani hukuncin kisa da aka yanke wa wasu mutanen kasar Ostareliya su biyu biyo bayan watsi da yin afuwa da shugaban kasar Joko Widodo ya yi kamar yadda lauyan da ke karesu ya bayyana a yau Talata.

Shugaba Widodo dai na kasar ta Indonesiya ya bayyana cewa babu gudu ba ja da baya a dangane da hukuncin kisan duk kuwa da irin kiraye-kiraye na shugabannin wasu kasashen waje da ya samu.

Todung Mulya Lubis lauyan da ke kare wadanda aka yankewa hukuncin, ya ce kamar yadda alkali ya fada watsin da shugaban kasar ya yi da yin afuwar ba wai doka bane saboda haka kotun ba ta da hurumi ta sake karbar bukatarsu.

Ya ce sun tsara daukaka kara tun daga yau Talata saboda haka dole kotu ta jinkirta yanke hukuncin da aka tsatra a wannan mako har sai an kammala bin duk wasu tanade-tanade da doka ta tsara.

Kasar Ostareliya dai na ci gaba da sa himma wajen ganin ba a kashe mata mutanennan nata ba guda biyu wato Myuran Sukumaran, 33, da Andrew Chan, 3, dukkaninsu dai an kamasu a shekarar 2005 kuma ana zarginsu ne da safarar hodar ibilis zuwa kasar ta Indonesiya.