Hukuncin daurin rai da rai a Najeriya | Labarai | DW | 09.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukuncin daurin rai da rai a Najeriya

Kimanin shekara guda bayan kai hari akan Ofishin hukumar zabe da wata Coci a Najeriya, kotu ta yankewa wanda ake zargi hukuncin daurin rai da rai.

Babbar kotun da ke Abuja ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga Shuaibu Abubakar daya daga cikin mutane hudun da ake zargi da laifin dasa bom da ya tarwatsa wata coci da kuma ofishin hukumar zabe a garin Suleja na jihar Nija dake Tarayyar Najeriyar a shekara ta 2012 wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 19.

Wakilinmu Uwais Abubakar Idris ya ruwaito cewa, yayin da take yanke hukuncin, mai sharia'a Bilkisu Aliyu ta kuma zartas da hukuncin daurin shekaru 10 a kan Umar Ibrahim tare da sallamar Musa Adam saboda kotun tace ba'a same shi da wani laifi ba.

Haka nan ma kamfanin dillancin labarai na Najeriyar ya ruwaito cewa kotun dake zamanta a Abuja ta samu mutanen da laifin shiryawa tare da kai hare-hare da bama-bami a ranara takwas ga watan Afirilun shekara ta 2012 kan ofishin Hukumar zabe da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 16 da kuma kai wani hari na daban da a kan wata Coci a ranar 10 ga watan Yuli na 2012 inda mutane 3 suka rasa rayukansu.

Rahotanni sun bayyana cewa ana kyautata zaton mutanen hudu 'yan kungiyar Boko Haram ne da ke gwagwarmaya da makamai a arewacin Najeriyar.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu