Hukuncin dauri ga shugaban kungiyar Mend | Labarai | DW | 21.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukuncin dauri ga shugaban kungiyar Mend

Tun bayan da hukumomin kasar Afrika ta Kudu suka danke shugaban kungiyar Mend,Henry Okah,jama'an Najeiya ke zaman jiron jin sakamakon hukuncin da za a yanke masa.

default

Tabbatar da aikata laifin da kotun ta yi a kan Henry Okah da ta same shi da laifufuka dai dai har 13 ya kasance muhimmin lamari a kan wannan shari'a da take daukan hankalin alummar Najeriyar, musamman sanin irin yadda bama vama da aka tabbatar da Henry Okah ne ya dasa su suka yi dalilin mutuwar mutane 12 da ma sauya bikin da aka fara a ranar ya koma juyayi, bakin ciki da ma al'ajabi.

Kodayake ya musanta cewar yana da hannu a harin to sai dai kungiyar ta Mend ta dage cewar lallai ita ce ta kai harin a yayinda shugaban Najeriya ya tsalle gefe guda yace ya san wadanda suka kai harin a wancan lokaci. To shin me wannan ke nunawa ne ga yadda shari'ar ta kasance? Malam Bashir Baba mai sharhi ne a kan al'ammuran yau da kullum a Najeriyar.

"Tun lokacin da aka yi wancan al'amari shugaba Goodluck Jonathan ya fito yana cewa an ce kungiyar Mend ne suka yi kuma Menda sun fito da bakinsu sun ce su suka yi, amma shi yace A'a . Ga mutumin da wasu zasu ce su suka yi amma shi ya fito yace bas u suka yi ba to si yasan wadnada suka yi kenan. Darasi a nan shine shugaba ni su iya bakinsu domin duk wanda aka ce shi shugaban jama'a ne ya san yadda zai iya bakinsa, don an ce baki shi kan yanka wuya, kuma kasan shi harshe das hi ake batawa kuma das hi ake gyarawa".

Ganin yadda cikin kasa da shekaru biyu da kame Henry Okah har aka kaiga kamala dukkanin bincike tare da tabbatar da cewar ya aikata laifin da ya musanta, a dai dai lokacin da sauran mutanen da aka kame a kan wannan laifi musamman kaninsa watau Charles Okar wanda har yanzu ake fafata shari'arsu ya sanya tambayar tasirin da wanna ka iya yi a yakin da Najeriya ke cewa tana yi da ta'adanci. Dr Usman Mohammed shine shugaban kungiyar kula da harkokin yan majalisu ta Afrika da ke Abuja.

‘'Hazaka da bincike da tsaya tukuru na irin kotuna na Afrika ta kudu wajen bincike cikin hanzari a kan lokaci ba tare da wani bata lokaci ba. Sannan kuma tunda ya shafi kasa da kasa su fito suka fayyace yadda al'ammari yake suka ba mai gaskiya gaskiya kuma mara gaskiya sun same shi da rashin gaskiya''.

To saidai ga Barrister Mohammed Tola kwarren lauya da ke Najeriyar yace akwai abubuwan da ya kamata a yi la'akari dasu a kan bukatar hanzarin shari'a a cikin Najeriya.

Mawallafa: Uwaisu Abubakar Idris/ Issoufou Mamane

Edita : Mahamadou Awal Balarabe