Hukuncin dauri a kan magoya bayan Mursi | Labarai | DW | 04.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukuncin dauri a kan magoya bayan Mursi

Gwamnatin wucin gadin Masar ta fara daukar matakin shari'a a kan dimbin magoya bayan Mursi dake tsare.

Kotun soji a ƙasar Masar ta yanke hukunci kan mutane 56 dake goyon bayan tsohon shugaba Muhammed Mursi. An dai yanke wa 11 daga cikin mutanen dauri na shekaru 25 a gidan kaso, sauran 45 kuwa kotun ta yanke musu daurin shekaru biyar. An dai zargi mutanen da laifin kai wa sojoji farmaki. Bayan yanke hukuncin ne shugaban ƙasar Adly Mansour yayi hira da manema labarai a gidan telebijin din ƙasar, inda yace babban abin da yasa a gaba shi ne dawo da zaman lafiya da kuma farfado da tattalin arzikin ƙasar.

Mawallafi : Usman Shehu Shehu
Edita : Saleh Umar Saleh