Hukunci akan kisan kai don kare mutuncin iyali | Siyasa | DW | 13.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Hukunci akan kisan kai don kare mutuncin iyali

A yau wata kotu ta yanke hukuncin daurin shekaru goma akan wani matashin da ya kashe yarsa wai don kare mutuncin danginsa

Ayhan Sürücü

Ayhan Sürücü

Wannan hukunci ne mai tsananin gaske alkalan kotun ta Berlin suka yanke idan aka kwatanta da yanayin rayuwa a nan kasar ta Jamus. Hukuncin dai ya tanadi daurin kusan shekaru goma a kurkuku ga wannan matashi Baturke, wanda ya kashe yarsa Hatun saboda ƙyamar salon rayuwarta. Kashe mutum saboda ƙyamar salon rayuwarsa da kuma ikirarin kare mutuncin dangi abu ne da alƙalai a nan ƙasar Jamus ba zasu taɓa amincewa da shi ba kuma a sabili da haka ne suka yanke wannan hukunci mai tsanani. To sai dai kuma shi kansa zaman shari’ar da aka yi ba tsage ainifin gaskiyar dalilin wannan danyyen aiki ba. Shin kisan na da nasaba ne da rashin fahimtar addinin musulunci ko kuwa wata matsala ce da ta shafi yanayin zamantakewar iyali da kuma dangin masu alhakin kisan? Abu ɗaya da aka hakikance da shi shi ne kasancewar wannan ba shi ne karo na farko da aka fuskanci irin wannan ɗanyyen aiki na kisan kai da sunan kare mutuncin iyali da dangi ba, hatta a nan Jamus. Alƙaluma na MDD sun ƙiyasce cewar mata kimanin dubu biyar ke fuskantar irin wannan kisa a sassa daban-daban na duniya a duk shekara. Kisan kai da sunan kare mutuncin dangi dai a hakika ba ya da wata nasaba da addinin musulunci, lamari ne da ya shafi tsarin zamantakewar iyalai masu ƙaramin ƙarfi. A sakamakon haka bai kamata a yi amfani da wannan matsala domin bata sunan miliyoyin musulmi dake zaune a nan ƙasar ta Jamus ba, musamman ma a daidai wannan lokacin da ake fama da mahawara a game da yadda za a iya kyautata zaman cuɗe-ni-in-cuɗeka tsakanin baƙi ‘yan kaka-gida, waɗanda akasarinsu musulmi ne, da kuma takwarorinsu Jamusawa. Ita kanta tafiyar hawainiyar da ake fama da ita a game da wannan batu, ‘yan siyasa ne ke da alhakinta. Domin kuwa har yau Jamus bata da wata nagartacciyar manufa dangane da zaman baƙi ‘yan kaka-gida a ƙasar. An yi tsawon shekaru da dama jami’an siyasar, musamman daga ɓangaren ‘yan mazan jiya, waɗanda suka daɗe suna ikirarin cewar wai Jamus ba dandalin kaka-gida ba ce. Wannan matsayi da ‘yan siyasar suka ɗauka shi ne ya sanya baƙi suka kasa sakin jikinsu a ƙasar ballantana su nemi sajewa da takwarorinsu Jamusawa. Waɗannan baƙi sun zama tamkar saniyar ware ne a harkokin rayuwa ta yau da kullum a kasar. Wajibi ne kuwa a samu canji ga lamarin. Wajibi ne kuma ‘yan siyasar Jamus su fahimci cewar waɗannan baƙi tamkar ƙarin arziki ne ga ƙasarsu, wacce a yanzu haka take fama da koma bayan haifuwa. Akwai bukatar ɗaukar nagartattun matakai domin kyautata makomar rayuwar tsattsan baƙin da aka haife su a nan Jamus, a fannoni na ilimi da sana’o’i na hannu daidai da ‘ya’yan Jamusawa, saboda ta haka ne kawai al’amura zasu daidaita a samu kyakkyawan zama na cuɗe-ni-in-cuɗe-ka tsakanin illahirin jinsuna da ƙabilun da ƙasar ta Jamus ta ƙunsa.