Hukunci akan Chodorkowski | Siyasa | DW | 28.12.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Hukunci akan Chodorkowski

A haƙiƙa hukuncin da aka yanke wa Chodorkovski da Lebedyev ba wani abin mamaki game da shi.

Mikhail Chodorkowski

Mikhail Chodorkowski

"Babu wani zance na adalci da kamanta gaskiya a wannan shari'a, wadda shari'a ce ta siyasa da aka zayyana mata umarninta. Kuma ko da yake ba a fito fili aka bayyana girman hukuncin ba, amma a zahiri yake cewar Chodorkovski da Lebedyev, aƙalla zasu ci gaba da zama a gidan kurkuku har ya zuwa tsakiyar shekara ta 2012, wato dai zuwa ƙarshen zaɓen shugaban ƙasar Rasha da za a gudanar wajejen farkon shekara ta 2012. Kai mai yiwuwa ma har ya zuwa shekara ta 2017.

Wani muhimmin abin da ake kyautata zato game da shari'ar karo na biyu akan Chodorkovski da Lebeyev shi ne kasancewar tsofon shugaban Rasha kuma Piraministanta na yanzu Vlamir Putin na da hannu dumu-dumu a hukuncin da aka zartas. Tun bayan kame 'yan kasuwan man na Rasha su biyu sama da shekaru biyu da suka wuce ake yayata maganar cewa Putin na ƙoƙarin jan kunnen Chodorkovski ne saboda shisshigin da yayi a harkar siyasar Rasha da kuma ƙalubalantar Putin. Ta haka tsofon shugaban na Rasha ya ɗauki Chodorkovski a matsayin wani babban abokin gabarsa, wanda ba ya sha'awar yi masa wani sassauci bisa manufa. Wannan maganar kuwa tayi daidai da buƙatar da Putin ya nunar a baya-bayan nan game da ganin an yanke hukunci akan Chodorkovski a cikin gaggawa. Yin hakan kuwa babban kuskure ne saboda shuagabannin Rasha sun daɗe suna bakin ƙoƙarinsu wajen nuna wa duniya cewar shari'ar da ake yi shari'a ce ta adalci. Domin magance wannan kuskure ne ya sanya shugaba Medvedev, a ƙarshen makon da ya gabata, ya fito fili yana mai cewar ba wani babban jami'in gwamnati dake da ikon furta wani abu akan wata shari'ar da ba a kawo ƙarshenta ba. Abin nufi a nan kuwa shi ne Vladmir Putin. Mai yiwuwa shugaban yayi hangen nesa ne a game da irin abubuwan da zasu biyu bayan hukuncin da za a zartas, wanda ya zama tamkar babban koma baya ga ƙoƙarin da shugaba Medvedev ke yi na sabunta al'amuran Rasha kuma babban cikas ga dangantakar Rasha da ƙasashen yammaci. Tuni dai shari'ar ta Chodorkovski ta zama wata alama ta rashin gaskiya da adalci a siyasar Rasha. Kai hatta a Rashan kanta 'yan kasuwan biyu Mikhail Chodorkovski da Platon Lebedyev tuni suka zama wata alama ta fafutukar neman adalci da tabbatar da gaskiya da mulkin demoƙraɗiyya a siyasar ƙasar."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu