1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumomin Najeriya sun ce Boko Haram na ƙarfafa hulɗa da ƙungiyoyin ƙetare

November 5, 2012

Ko da yake ana zargin cewa wasu 'ya'yan ƙungiyar sun samu horo wajen ƙungiyar al-Qaida reshen Magrib, amma ba a santa da wata alaƙa da kungiyoyin ƙetare ba.

https://p.dw.com/p/16dIL
Hoto: AP

Mai ba wa shugaban Najeriya shawara a kan harkokin tsaron ƙasa Sambo Dasuki ya ce ƙungiyar nan da ake kira Boko Haram ta na ƙara ƙarfafa hulɗa da wasu ƙungiyoyi masu zazzafan ra'ayi na wasu ƙasashen Afirka. Dasuki ya faɗa wa wani babban taro kan tsaron yankin yammacin Afirka cewa babbar damuwarsu a yanzu shi ne ƙarin haɗin kai da ake samu tsakanin ƙungiyar ta Boko Haram a Najeriya da ƙungiyoyin 'yan ta'adda da suka zauna da gindinsu a yankin Sahel. Ana zargin cewa wasu 'ya'yan ƙungiyar ta Boko Haram sun samu horo a hannun ƙungiyar al-Qaida reshen arewacin Afirka musamman a arewacin Mali, sai dai kawo yanzu ba a san ƙungiyar da wata alaƙa da ƙungiyoyin ƙetare ba. Dasukin dai bai yi bayani dalla dalla kan wannan batu ba.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu