Hukumomin Mali sun kama Amadou Sonogo | Labarai | DW | 28.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumomin Mali sun kama Amadou Sonogo

Mahukuntan Mali sun kama tsohon shugaban mulkin sojin kasar Kaftin Ahmadou Haya Sanogo bayan da ya bijirewa wani sammaci da wata kotun kasar ta aike masa.

Mali's junta leader Captain Amadou Sanogo speaks during a new news conference at his headquarters in Kati April 3, 2012. REUTERS/Luc Gnago (MALI - Tags: POLITICS MILITARY)

Kaftin Amadou Haya Sanogo

Rahotanni daga kasar Mali na cewar hukumomi sun tsare tsohon shugaban mulkin sojin kasar Kaftin Amadou Haya Sanogo inda ake zarginsa da bacewar wani kanar na rundunar sojin Mali din da ma rasuwar wasu soji su shidda.

A jiya Laraba ce dai mahukuntan kasar suka ce an kame Kaftin Sanogo bayan da ya yi watsi da sammacin da wato kotun kasar ta aike masa na ya bayanna gabatan domin yin cikakken bayani game da bacewar kanar din lokacin da soji suka yi wata zanga-zanga cikin watan Satumbar da ta gabata.

Dama dai kungiyoyi na kare hakkin bani adama a cikin da wajen Mali din sun zargi dakarun kasar da amfani da karfin da ya wuce kima wajen azabtar da mutane da ma dai bacewar da dama daga cikinsu.

Tuni dai al'ummar kasar suka fara bayyana ra'yoyinsu mabanbanta dangane da wannan kamu da yi wa Sanogo inda wasu ke hasashen hakan ka iya dagula lamura a kasar wadda dama ta ke cikin tsaka mai wuya.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu