Hukumomin Kenya na gudanar da bincike | Labarai | DW | 25.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumomin Kenya na gudanar da bincike

Ministan cikin gida na ƙasar ya ce ƙasashen duniya waɗanda suka haɗa da Ingila da Amirka da Isra'ila da Jamus da kuma Canada na taimaka musu wajen gudanar da bincike.

jami'an na yin binciken ne domin gano sauran gawarwaki da sauran bama-bamai watakila, waɗanda basu tashi ba a cikin kanti nan na Westgate wanda 'yan ƙungiyar Al-Shabaab suka kai hari a kansa tun ran Asabar.

Ministan josephe Ole Lenku ya ce za a ɗauki lokaci ana gudanar da aikin na bincike kusan mako guda. Gwamnatin ta Kenya ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku domin yin alhini na asarar rayukan da aka samu na mutane 61 kana sama da ɗari biyu suka jikkata. Ƙungiyar ta Al-Shabaab a kan shafinta na Twitter ta ce mutane 137 suka mutu.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh