Hukumomin Kanada suna farautar ′yan bindiga | Labarai | DW | 22.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumomin Kanada suna farautar 'yan bindiga

Wani dan bindiga ya yi harbi a majalisar dokokin kasar Kanada

An rufe majalisar dokokin kasar Kanada bayan wani dan bindiga ya yi harbi, lokacin da Firaministan kasar Stephen Harper ya ke cikin majalisar. An fice da firamnistan kuma an karfafa matakan tsaro. Tuni 'yan sanda suka mamaye majalisar dokokin da ke Ottawa fadar gwamnatin kasar.

Tun farko wani dan bindiga ya harbe wani soji a wata makabarta ta sojoji. An rufe daukacin barikokin soji da ke kasar ta Kanada ga fararen hula sakamakon matakan tsaro da aka karfafa. Ranar Litinin wani sabon Musulunta ya kade wasu sojoji biyu da mota, inda daya ya hallaka sannan daya kuma ya samu raunika, kafin 'yan sanda su bindige matukin motar. 'Yan kasar kasar ta Kanada sun tabbatar da cewa Firamnista Stephen Harper yana cikin koshin lafiya, bayan ficewa da shi daga wajen da aka yi harbi a majalisar dokokin kasar.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Pinado Abdu Waba