1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gano kabari dauke da mutane 200 a Habasha

Suleiman Babayo MNA
November 9, 2018

'Yan sanda na bincike sakamakon bankado kabari dauke da gawawwaki kimanin 200 a gabashin kasar Habasha abin da ake dangantawa da wani tsohon babban jami'in yankin da yake tsare a hannun hukumomi.

https://p.dw.com/p/37w1I
PM  Abiy Ahmed  in der Frankfurt Arena
Hoto: DW/M. Zimmer

'Yan sandan kasar Habasha sun gano wani kabari da ke dauke da gawawwaki kimanin 200 a yankin gabashin kasar. Kafar yada labarai ta kasar ta ce 'yan sandan suna aiki ne game da umurnin kotu kan amfani da hanyar da ta saba doka da ake yi wa tsohon shugaban yankin Habasha mai magana da harshin Somali, Abdi Mohammed wanda yanzu haka yake tsere.

Hukumomi sun bayar da kwanaki 14 domin yin binciken kwayoyin halitta kan gawawwakin da aka tono. Babu tabbacin wuraren da mutanen da suka fito da abin da ya faru da su.

Tashe-tashen hankula masu nasaba da kabilanci na zama babban kalubale ga Firaminista Abiy Ahmed mai ra'ayin kawo sauye-sauye da ya dauki madafun ikon kasar ta Habasha da ke gabashin Afirka a watan Afrilun wannan shekara ta 2018.