Hukumar zaɓe a Madagaska ta tsaida ranar zaɓe | Labarai | DW | 23.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumar zaɓe a Madagaska ta tsaida ranar zaɓe

Za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a ranar 25 ga watan Oktoba da ke tafe, kana ta ce ce a yi zaɓen 'yan majalisun dokoki a rana 20 ga watan Disamba.

Wannan shi ne karo na uku kennan da hukumar ke ɗage zaɓen wanda a wannan jiƙon ta ce, ta yi hakan ne domin ta kawo gyara ga rejistar 'yan takarar guda uku da ta soke waɗanda za su tsaya a zaɓen shugaban ƙasar.

Waɗanda suka haɗa da Andry Rajoelina shugaban wucin gadin, da uwargidan tsohon shugaban ƙasar Marc Ravalomanana da kuma tsohon shugaban ƙasar Didier Ratsiraka. Wanan zaɓe dai zai kwo ƙarshen rikicin siyasar da aka kwashe kusan shekaru fuɗu da rabi ana yi a ƙasar tun bayan faɗuwar gwamnatin Marc Ravalomanana a shekarun 2009.

Mawalllafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman