Hukumar OPCW ta kammala aikinta a Siriya
October 31, 2013Hukumar OPCW ta ce wurarare guda biyu ne kawai jami'anta ba su sami sukunin kai wa ba garesu saboda dalilai na tsaro.
A cikin watan Satumba da ya gabata Siriya ta amince ta lalata makaman nata, bayan wata yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Amirka da Rasa domin kaucewa kai wa ƙasar hare-hare na taron dangi, dangane da zargin da ake yi mata da yin amfani da makaman a kan farar hula. A gobe ne ɗaya ga watan Nuwamba wa'adin da MDD ta ebawa hukumar domin kammala aikin yake ƙarewa. Kuma nan gaba a ranar 15 ga watan da ke kamawa hukumomin Siriya da na hukumar ta OPCW za su shiga mataki na biyu na aikin lalata makaman masu guba na kusan ton 1000 da Siriya ta ke da shi na makamin Sarin.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu