Hukumar Interpol ta kama magunguna na jabu | Labarai | DW | 18.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumar Interpol ta kama magunguna na jabu

Hukumar da ke kula da hulda tsakanin 'yan sanda a duniya ta Interpol, ta sanar da cafke wasu magunguna na jabu fiye da miliyan 20 a sassa daban daban na duniya.

Cibiyar Interpol a Lyon

Cibiyar Interpol a Lyon

Hakan ta faru ne bayan gudanar da wani babban bincike da ya hada 'yan sanda na kasashe 115 daga ranar 9 zuwa ran 16 ga wannan wata na Yuni, wanda aka kira "Operation Pangea VIII " da ya bada damar kama mutane 156 da ake zagi da hannu cikin lamari a fadin duniya. Hukumar ta Interpol mai cibiya a birnin Lyon na kasar Faransa cikin wata sanarwa, ta ce magungunan sun kai na kudi Euro miliyan 71 wanda kuma shi ne kamu mafi girma tun bayan da suka fara wannan aiki na hadin gwiwa.

A hannu daya kuma ayyukan na hadin gwiwa na 'yan sandan duniya, ya sanya dakatar da wasu tallace-tallace akalla 550 na magunguna na jabu da ake yi ta shafin Internet, tare da rufe wasu shafukan na Internet din akalla 2,400.