Hukumar CENI a Chadi ta ɗage ranar zaɓe | Labarai | DW | 27.09.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumar CENI a Chadi ta ɗage ranar zaɓe

Hukumar zaɓen a ƙasar Chadi ta bayyana saban jaddawalin zaɓɓuɓukan da za a shirya shekara mai zuwa.

default

Shugaban ƙasar Chadi Idriss Deby Itno

Hukumar zaɓen ƙasar Chadi  ta ɗage zaɓukan shugaban ƙasa,na majalisar dokoki da ƙananan hukumomin zuwa shekarar 2011 sakamakon matsalolin shirye-shirye.

Hukumar zaɓen ta bayyana cewa a saban jaddawalin zaɓen, za a gudanar da zaɓen majalisar dokoki a ranar 20 ga watar Febrairu, na ƙananan hukumomi kuma 27 ga watan Maris kana a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa zagaye na farko a ran takwas ga watan Mayun 2011.

Jaddawalin farko ya tanadi shirya zaɓɓuɓkan ´yan majalisa da na ƙananan hukumomi kamin ƙarshen shekara da mu ke ciki.

Baki ɗaya, mutane miliyan huɗu da rabi ne, ya cencenta su kaɗa ƙuri´a a wannan zaɓɓuɓuka.

Mawallafi: Pinaɗo Abdu

Edita: Yahouza Sadissou Madobi