Hugo Chavez na fama da matsalolin nunfashi | Labarai | DW | 04.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hugo Chavez na fama da matsalolin nunfashi

Gwamnatin Venezuela ta ce shugaba Hugo Chavez ya fara dawowa cikin hayyacinsa bayan fiɗar huhu da likitoci su ka yi masa.

****ARCHIVBILD****Venezuela's President Hugo Chavez, left, hugs a hospital worker, back to camera, during a visit to injured people after a refinery explosion at the Rafael Calle Sierra's public hospital in Punto Fijo, Venezuela, Monday, Aug. 27, 2012. A fire at the Amuay refinery spread to a third fuel tank on Monday nearly three days after a powerful explosion that killed 41 people and ignited the blaze, Vice President Elias Jaua said. (Foto:Ariana Cubillos/AP/dapd)

Hugo Chavez na godiya ga likita

Gwamnatin ƙasar Venezuela ta ce an magance matsalolin nunfashi da Shugaba Hugo Chavez ya yi fama, sakamakon cutar huhu da ya fuskanta.

Ministan yaɗa labaran ƙasar Ernesto Villegas, wanda ya yi bayani kan halin da shugaban ke ciki, cikin wata sanarwar da ya karanta da yammacin jiya Alhamis, ya ce, cutar huhu da shugaba Chavez ya samu, ta janyo masa matsalolin nunfashi, kuma tawogar likitocinsa sun yi aiki akai.

Shugaban ƙasar ta Venezuela Hugo Chavez ɗan shekaru 58 da haihuwa, an yi masa aikin fiɗan cutar sankara karo hudu a ƙasar Kuba, ranar 11 ga watan Disamban da ya gabata. Kuma bisa tsarin ƙasar ranar goma ga wannan wata na Janairu za a rantsar da shi, domin fara wa'adin mulki sakamakon lashe zaɓen watan Oktoba da ya gabata.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Yahouza Sadissou Madobi