Huɗubar Paparoma Benedikt na 16
February 13, 2013Paparoma Benedikt na 16 ya hallara a karon farko a baiyanar jama'a a birnin Roma na Italiya tun bayan baiyana aniyarsa ta yi murabus. Baya ga huduba da ya sa ba yi, yayi karin haske game da dalilansa na sauka da kujerar shugabancin darikar romankatolika ta duniya. gaban dubban kiristoci da suka hallara a fadarsa,Benedikt na 16 ya ce ya yanke wannan shawarar saboda ci gaba darikar ta roman katolika. Tun da farko dai ya nunar da cewa ba shi da karfin sauke nauyin da ya rataya masa a wuya yadda ya kamata saboda yawan shekaru. Paproma mai murabus ya yi wa kiristocin duniya godiya game da fahimtar wannan mawuyacin mataki da ya dauka. kana ya nemesu su ci gaba da yi masa adu'a da ma dai wanda zain maye gurbinsa. A ranar litin da ta gabata ne Benedikt na 16 ya baiyana cewa zai yi murabus a ranar 28 ga watan Fabrairu mai zuwa.
Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita:Yahouza Sadissou Madobi