HRW: Ana take hakkin dan Adam a Najeriya | Labarai | DW | 13.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

HRW: Ana take hakkin dan Adam a Najeriya

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Rights Watch a rahoton da ta fitar na shekara shekara ta soki lamirin mahukuntan Najeriya da tursasawa da kuma rashin martaba hakkokin bil Adama.

Kungiyar ta ce a shekarar da ta gabata ta 2016 al'amuran take hakkin dan Adam sun cigaba da wakana musamman daga bangaren jami'an tsaro wadanda ya kamata su martaba doka da kare hakkin al'umma.

Ta ce a kudu maso gabashin Najeriya yan sanda sun hallaka masu rajin Biafra su kimanin 40 a yayin wata zanga zanga da yan kungiyar suka yi a tsakanin watan Fabrariru da watan Maris.

Haka kuma kungiyar ta Human Rights Watch ta ce a watan Disambar 2015 sojojin sun hallaka yan kungiyar yan uwa musulmi su 347 a garin zaria tare da jikata wasu da dama.

Bugu da kari Human Rights Watch ta yi kira ga gwamnatin Najeriya ta martaba kundin tsarin mulki ta kuma yi biyayya ga umarnin kotu wadda ta bukaci a saki shugaban kungiyar ta yan uwa musulmi Ibrahim El Zakzaki tare da matarsa wadanda hukumomi ke cigaba da tsare su ba tare da gurfanar da su gaban shari'a ba lamarin da ta ce ya saba dokar kasa da kasa.