1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu tabin hankali na rayuwa cikin kunci

Ramatu Garba Baba
October 6, 2020

Kungiyar kare hakin bil'Adama ta Human Rights Watch, ta ce dubban mata da yara kanana ne ke rayuwa cikin mummunan yanayi a wasu cibiyoyin da aka tanadar da sunan kulawa da masu tabin hankali a sassan duniya.

https://p.dw.com/p/3jTx2
Bildergalerie Psychisch Kranke in Afghanistan
Hoto: Aref Karimi/AFP/Getty Images

Kungiyar kare hakin bil'Adama ta Human Rights Watch, ta ce ta gano mummunan yanayin da wadansu cibiyoyi masu kula da masu tabin hankali ke ciki a sassan duniya. A rahoton Kungiyar na wannan Talatar, ya baiyana yadda marasa lafiya ke zama babu abinci da rayuwa cikin kazanta , wasunsu an garkame su da sarka a yayin da ake ci gaba da gana musu azaba.

Binciken ya ce, mata da yara kanana na cikin wannan mummunar yanayi a kasashen duniya kimanin sittin, Najeriya na daya daga cikin kasashen da ake fuskantar karancin cibiyoyin da asibitocin lura da masu tabin hankali sai kuma kasashen Chaina da Mexiko inji Human Rights.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da ake shirin gudanar da ranar Lafiya kwakwalwa ta duniya da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe don tunawa da masu tabin hankali, ana dai gudanar da bikin ne a ranar goma ga watan Oktoban kowacce shekara.