Zanga-zanga na kara kamari a Hong-Kong
June 12, 2019Talla
'Yan sanda a kasar Hong-Kong sun yi amfani da barkonon tsohuwa da kulake da ma harsasan roba wajen tarwatsa masu zanga-zangar da suka yi yinkurin kutsawa a cikin zauren majalisar dokokin kasar inda 'yan majalisar ke shirin nazarin dokar kafin sanya mata hannu.
Masu zanga-zangar wadanda akasarinsu matasa ne sanye da bakaken riguna da kuma lemomin ruwa sun yi ta dauki ba dadi har ma da bai wa hammata iska da 'yan sandan a gaban harabar majalisar, lamarin da ya tilasta wa Shugaban majalisar dage zaman muhawarar zuwa wani lokaci a nan gaba.
Sai dai gwamnatin kasar ta Hong-Kong ta ce batun ta janye dokar kamar yadda masu zanga-zangar ke bukata sam bai taso ba. Mahukuntan kasar sun ce 'yan sanda 22 sun ji rauni a cikin fadan