Arangama da masu zanga-zanga a Hong Kong
September 21, 2019Talla
Jami'an tsaron a Hong Kong sun yi amfani da kulake da hayaki mai sha kwalla da ruwan zafi don tarwatsa dandazon masu boren, da suka ja daga ta hanyar kafa shingaye a birnin Tuwen Mun da ke arewa maso gabashin Hong Kong, kana kuma tuni jamai'an suka damke masu zanga-zangar da dama. Rahotanni sun ce yanzu hakan ma masu boren na ci gaba da kai ruwa rana tsakaninsu da jami'an tsaro da ke bukatar ta ko halin kaka su dakile zanga-zangar.