1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalubalen masu zanga-zangar Hong Kong

Zulaiha Abubakar
November 19, 2019

Masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin Hong Kong da ke zaune a cikin jami'ar da jami'an 'yan sandan kasar suka yi wa kaawanya, na neman mafita, dangane da matsalar karancin abinci da suka fara fuskanta.

https://p.dw.com/p/3TJ56
Honkong Proteste Polytechnische Universität | Versorgung
Hoto: Reuters/A. Abidi

Jami'an tsaron dai sun shiga rana ta uku da kewaye jami'ar yankin Hong Kong din. rahotanni sun nunar da cewa 600 daga cikin masu zanga-zangar sun fice cikin lumana, inda wasu da dama suka yi watsi da gargadin mahukuntan tare da ci gaba da kasancewa a harabar jami'ar.

Mazauna yankin dai sun bayyana fargaba game da makomar masu zanga-zangar da suke ja da hukuma daga cikin jami'ar, ko da yake jagorar yankin Carrie Lam ta shaidawa manema labarai cewa gwamnati za ta yi kokarin ganin sauran masu zanga-zangar sun fice cikin lumana.