1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakile masu zanga-zanga a Hong Kong

Binta Aliyu Zurmi
November 20, 2019

Rahotanni daga Hong Kong na nuni da cewar 'yan sanda na ci gaba da yi wa jami'ar birnin kawanya, inda suke jiran masu zanga-zanga da su mika kansu.

https://p.dw.com/p/3TNks
Hongkong Demonstranten versuchen die Polytechnische Universität zu verlassen
Hoto: AFP/A. Wallace

Wasu daliban jami'ar da ke tsare a ciki na samun taimakon wadanda ke waje ta hanyar kokarin fiddo su da igoyoyi, wasunsu kuma sun bi ta wata magudanar ruwa da ta kai tsawon kilomita guda domin gujewa kamun 'yan sandan. An sami labarin cewa har yanzu akwai masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin da ke cikin jami'ar a makale, yayin da rahotanni ke cewar an kama wasu daga cikinsu. 

A kokarin damke wadanda suka rage a cikin jami'ar, jami'an tsaro na amfani da barkonon tsohuwa domin tilasta musu fitowa daga cikin ginin jami'ar da suka buya.