Hong Kong: An fara kawar da shingaye a sansanin zanga-zanga | Labarai | DW | 18.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hong Kong: An fara kawar da shingaye a sansanin zanga-zanga

A cewar wasu masu zanga-zangar masu kawar da shingayen sun wuce gona da iri inda suke kawar da wasu shingayen da ba kotu ta ce a kawar da suba.

Mahukunta a Hong Kong a ranar Talatannan sun fara kawar da shingaye da sauran komatsai da aka dasa a wasu daga cikin filaye da daliban kasar suka gudanar da zanga-zanagar neman kafa dimokradiya da ta dauki hankalin duniya, wacce kuma ta tsaida harkokin kasuwanci na tsawon wani lokaci a wannan birni.

Babu dai wata babbar turjiya da ake fiskanta a yayin wannan aiki da zai bada damar gudanar da harkoki.

Akwai jami'an 'yan sanda da suke sanya idanu ga maaikatan da suke gudanar da wannan aiki a gaban wani katafaren gini mai hawa 33 na CITIC, bayan da mai ginin ya samu dama daga kotu da ta bada umarnin a kawar shingayen, amma daga cikin wasu masu zanga-zangar sun rika hayaniya inda suka ce masu kawar da shingayen sun wuce gona da iri inda suke kawar da wasu shingayen da aka kafa a kusa da wani shataletale inda daliban ke cewa wurin baya cikin wurin da kotu ta bada umarni.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu