1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Kallon fina-finai ta manhaja

Ahmed Salisu LMJ
August 26, 2020

Wani matashi mai suna ya kirkiri wata manhaja da mutane kan yi amfani da ita wajen kallon fina-finan da ake yi a masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood da ke jihar Kano a Najeriya.

https://p.dw.com/p/3hWhf
Nigeria Kannywood
Manhaja domin kallon fina-finan masana'antar Kannywood da ke arewacin NajeriyaHoto: DW/I. Yakubu

Matashin mai suna Jamilu Abdusslam wanda ya karanci aikin jarida a Jami'ar Bayero da ke Kanon Najeriya, ya ce ya yi wannan yunkuri ne domin nemawa kansa abin yi sannan kuma ya taimaka wajen ganin takwarorinsa matasa na dogaro da kansu. Tuni dai kwalliya ta fara biyan kudin sabulu kamar yadda ya shaidawa DW. Kasancewar hannu daya baya iya daukar jinka, daga lokacin da Jamilu ya fara wannan aiki kawo yanzu, ya ja matasa da dama a jika domin su yi aikin tafiyar da wannan kamfani nasa na Northflix tare.

Wadannan matasa da yake aiki da su a matakai dabam-dabam da ma kuma irin alherin da ya samu daga sanda ya kirkiri wannan manhaja ta Northflix na daga cikin abubuwan da ya ce yana alfahari da su idan ana magana ta nasara. To sai dai duk da irin nasarorin da ya cimma, Jamilu ya ce akwai tarin matsaloli da suke fuskanta wajen tafiyar da wannan kamfani nasa. Guda kuwa daga ciki shi ne irin yadda wasu bata-gari ke kokarin rusa duk irin kokarin da suka yi, kafin su kawo ga wannan gaba da suke kai.

Yayin da suke kokarin dakushe yukurin masu yi musu kutse domin ganin dorewar kamfanin, Jamilu ya ce za su ci gaba da kasancewa kan matsayar da suke kai, inda ya ce ba zai karbi aikin gwamnati ba ko kuma na kamfani saboda ya fi ganewa tsayuwa da diga-digansa. Yanzu haka dai fatan Jamilu Abdussalam shi ne wannan kamfani nasa na Northflix, ya samu karbuwa ba wai a Najeriya ko nahiyar Afirka ba, har ma da sauran sassan duniya inda zai yi gogayya da wadanda ake da su da suke nuna fina-finai da ake shiryawa a masana'antar Bollywood da ke Indiya da kuma Hollywood da ke Amirka.