1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

HdM: Mai na’urar hada shayi a Gombe

April 6, 2022

Musa Muhammad wani matashi ne a Gombe wanda ke karatunsa na Boko a kwalejin kimiyya da Fasaha ta tarraya da ke Bauchi wanda ya kirkiri wata na’urar da ke hada sinadaran shayi kamar madara da sukari da sauransu.

https://p.dw.com/p/49Y7X
Kaffeemaschinen
Hoto: DW

Shi dai Musa Muhammad matashi ne da ke nemo wa masu sana'ar shayi hanyar da za ta saukake musu yadda za su yi sana'ar  tare da biya wa abokan huldarsu bukata. Musa Muhammad ya ce: " Wannan na'urar na hada shayi kofi hudu a minti daya, amma su, duk yadda suka yi ba zai hada Kofi biyu ba a minti daya.”

To wace nasara za a iya cewa Musa Muhammad ya samu sanadiyyar hada wannan na'ura wacce ke zama ta farko a wannan sashe na Najeriya? Ya ce: "Na samu na kammala hada wannan na'ura. Kuma sanadiyyar ta mun je wata gasa a Abuja wanda har muka ciwo wa jihar Gombe Lamba ta uku

Sai da Musa Muhammad yana gamuwa da kalubale musamman na samun irin na'urorin da yake so ya yi amfani da su, inda yake daukar lokaci kafin su iso gare shi. Sannan yana fuskantar kalubalen masu gidan rana ganin ba karfi yake da shi ba.

Masana kimiyya kamar Usman Muhammad Shehu sun yaba wa kokarin wannan matashi saboda fasahar da ya nuna, inda suka yi kira ga masu shayi da karfafi masa gwiwa ta hanyar sayen na'uorin.

Usman Muhammad Shehu ya ce: "Ba karamin kwazo ba ne, sannan kuma ya yi amfani da wannan baiwar wajen sarrafa na'ura wanda zai dinga hada kayan shayi. To ina jan hankalin matasa su yi koyi da irin sa. Ina jan hankalin Kungiyar masu shayi musamman shugabansu ya zo ya samu zama da wannan matashi a ga yadda za a yi a dinga amfani da wanan na'ura wajen masu shayi."

Shi dai Musa Muhammad ya ce da a ba shi aikin gwamnati gara ta tallafa masa ya kera na'urorin da yawa don shi ma ya samar wa matasa ayyukan yi, wanda hakan zai taimaki gwamnatin a kokarinta da rage marasa ayyukan yi.