1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hawlatu na so a bar mata su fara limanci

Mouhamadou Awal Balarabe
May 28, 2019

A Tamale na Ghana, malama Hawlatu Abdallah ta kalubalanci matsayin hana mata limanci a Musulunci, inda ta kafa kungiyar mata da ke yada Islama da nufin karfafa musu gwiwa don su jagoranci jam’u a masallatai dabam-dabam.

https://p.dw.com/p/3JJhx
Moschee in Kumasi, Ghana
Hoto: imago/D. Delimont

 Imam Mustapha Abdullahi ya saba jagorantar jam’u a masallaci Kpalsi da ke birnin Tamale na arewacin Ghana. Ya saba raba sahun maza da na mata da ke halartar sallar ta hanyar sanya labule tsakaninsu, saboda addini bai yarda su yi cudanya tsakaninsu ba, sannan kuma Islama ba ta amince mata su yi limanci ba. Malam Mustapha ya ce: "Jikin mace na da daraja saboda haka ne bai dace a yi cudanya da ita a lokacin sallah ba. Idan ka tsaya a kusa da ita, ba za ka samu nitsuwa a jam’u ba, Shi ya sa addininmu bai amince ba musamman idan matar ba taka ba ce . "

 Amma Hajiya Hawlatu Abdallah na son mayar da wannan tsari tarihi. Hasali ma a wannan wata mai alfarma na Ramadana, mata Musulmai da dama na halatar  wa'azi da take yi a kullum. Hasali ma Hajiya Hawlatu ta yi imanin cewa aikinta na fadakarwa na tasiri.
 Ta ce "Dalilin da ya sa nake koyar da 'yan uwana mata shi ne, na nakalci Alqur'ani, kuma ina so in karantar da su ilimin da Allah ya horemin."

Frauen beten in der Sehitlik-Moschee in Berlin
Hoto: Getty Images/O. Messinger

 Sannu a hankali mata sun fara bin koyawar Hawlatu sau da kafa, in ji Ayishetu Adams, wata mace da ke halartar wa'azi a kai a kai, inda ta ce "Tana koyar da mu yadda za mu kaskantar da kanmu. Idan aka kasance mai girman kai da rashin biyayya kuwa, tana bayyana cewa akwai ranar da za ku mutu. Idan kana yawan fada, tana sanar da kai cewa mummunan abu ne. "

Sai dai Imam Mustapha ya ce akwai mizanin da mace mai wa'azi bai kamata ta zarta ba a Islama. Ya ce "Ba a yarda mace ta yi wa'azi a bainin jama'a ba, ba a yarda ta jagorancin sallah ba. Wannan ya saba wa addini. Tana iya jagorantar mata kawai, amma ban da maza ba. "

An saba ganin mata na karatun Alkur'ani a Ghana. Amma suna fuskantar turjiya a masallatai wajen limanci. Sai dai wasu mata kamar su  Hamida Alhassan na ganin cewa lokaci ya yi da za a kawo sauyi. Ta ce "Ina da 'yar uta da ta yi saukar karatun Alkur'ani. Don haka ban ga dalilin da ya sa mace ba za ta iya jagorantar jam'u ba. Ina jin cewa mace na iya limanci saboda na ga wata mace da ke yi wa mata limanci. Inna tsammanin lokaci ya yi da za a ba wa matan da suke da sani damar yin limanci. "

Matan da ke da wannan bukata ba su taka kara sun karya ba tsakanin Musulmi Ghana.Saboda haka Hajiya Hawlatu na da jan aiki a gabanta wajen sa a yarda da mace a matsayin limamiya a kasar.