Hatsarin jirgin ruwa a Mali ya hallaka mutane 32 | Labarai | DW | 13.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hatsarin jirgin ruwa a Mali ya hallaka mutane 32

Yawan mutanen da suka mutu sakamakon hatsarin karamin jirgin ruwa a Mali sun kai 32.

Mutane 32 aka tabbatar da sun hallaka bisa hatsarin wani karamin jirgin ruwa a kogin da ke tsakiyar kasar Mali. Akwai kananan yara daga cikin wadanda suka mutu.

Jami'ai sun ce har yanzu ana ci gaba da aikin ceto, na yuwuwar samun sauran masu rai daga cikin wadanda suka bace. Tun farko an jingine aikin ceto cikin daren jiya, sannan aka koma da safiyar wannan Lahadi. Akwai mutane 210 da aka ceto da rai.

Jirgin ruwa yana kan hanyar garin zuwa Timbuktu daga Mopti, akwai nisan kilo-mita 700 tsakanin garuruwan. Lokacin da jirgin ruwan ya yi hatsari yana shake da mutane fiye da kima. Mahukuntan kasar ta Mali na fatar kara ceto wasu da rai.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu