1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hatsarin jirgin Habasha da na Lion Air sun yi kama

Abdoulaye Mamane Amadou MAB
March 17, 2019

Gwamnatin Habasha ta ce akwai kamanceceniya dangane da dalilan faduwar jirgin Boeing Max na Ehtiopian Airlines da Lion Air na Indonesiya: Sakamakon farko na binciken na'u'rorin nadar magana na jirgin ne ya gano haka.

https://p.dw.com/p/3FDbG
Boeing 737-800 Absturz Libanon
Hoto: AP

Binciken farko na na'urorin nadar bayanai na jirgin saman Habasa da yayi hadari a makon da ya gabata, ya yi nuni da cewar dalilan faduwar jirgin na kama da na kamfanin Lion Air na kasar Indonesiya da ya fadi a cikin watan Oktoban shekarar da ta gabata. 


Da yake magana da kafofin yada labarai, ministan sufurin kasar Habasha Dagmawit Moges ya ce sakamakon binciken farko na akwatin nadar bayyanan ya fito karara da irin matsalar da jirgin Indonesya Boeing MAX ya fuskanta, yana mai cewar kashin farko na cikakken rahoton za su samu ne nan da kwanaki 30 masu zuwa. 

A ranar goma ga wannan watan ne jirgin Habasha Boeing MAX dauke da mutane 157 ya fadi jim kadan bayan tashi daga Addis Ababa zuwa Nairobin Kenya, lamarin da ya sa kasashen duniya dabam-daban dakatar da amfani da shi har sai abin da hali ya yi.