Harrison Ford ya samu hadarin jirgi | Labarai | DW | 06.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harrison Ford ya samu hadarin jirgi

Shahararran dan wasan fim din nan na Amirka Harrison Ford ya samu rauni a sakamakon wani hadarin jirgi da ya samu.

Harrison Ford

Harrison Ford

Karamin jirgin da shi shahararran dan fim din ke tukawa, wanda ya ke tsofon jirgi ne na kawa tun na lokacin yakin duniya na biyu, ya samu matsalar inji ne jim kadan bayan ya tashi daga filin jirgin Santa Monica da ke Jihar Califoniya, inda matukin jirgin ya nemi saukar gaggawa a wani filin wasan kollon golf bayan da ya bugi wata itaciya, amma kuma masu aikin ceto sun sanar cewa dan fim din Harrison ford mai shekaru 72 da haihuwa, ya san inda yake bayan hadarin, kuma yana iya managa. A halin yanzu dai yana a wani babban asibiti inda ake kula da lafiyarsa, kuma likitoci sun sanar cewa raunukan da ya samu ba su sanya rayuwarsa cikin hadari ba.