HARKOKIN SIYASAR KASAR IRAQI. | Siyasa | DW | 08.12.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

HARKOKIN SIYASAR KASAR IRAQI.

HOTON SHUGABA BUSH DAYA JAGORANCI KAIWA IRAQI HARIN SOJI.

default

A yayin da rikice rikice da tashe tashen hankula ke kara kamari a iraq a dai dai lokacin ne kuma mahukuntan kasar da hukumar zabe ke kara nazarin yanayin yadda za a gudanar da zaben gama gari da suka shirya yi a karshen watan najairun sabuwar shekara.

A masali rahotanni daga kasar sun tabbatar da cewa wasu yan fadan sari ka noke da yan bindiga dadi sun kai wani mummunan hari a yankin yan darikar sunni dake arewa maso yammacin birnin Bagadaza a yau laraba.

Hakan yayi sanadiyyar jiwa wasu mutane fararen hula raunuka iri daban daban wasu kuma ya haifar m,usu da rasa ransu baki daya.

Ba a da bayan haka akwai kuma bayanan rashin zaman lafiya daga wasu yankunan na iraqi da daman daban kama dai daga Falluja da Mosul da Baiji da ire iren makaman tansu.

To amma duk da wan nan hali da ake ciki mahukuntan kasar ta iraqi na ganin cewa gudanar da wan nan zabe kamar yadda aka tsara shi shiya fi a maimakon jinkirtashi izuwa wani lokaci a nan gaba.

A yanzu haka dai da yawa daga cikin jamiyyun kasar ta iraqi da kuma wasu manya manyan kabilun kasar sun fito fili sun nuna bukatar su ta a dage wan nan zabe har zuwa lokacin da harkokin tsaro zasu inganta a fadin kasar baki daya.

To amma duk da wan nan kira da wadan nan jamiyyu sukayi gwamnatin kasar tayi buris,babu ma abin da tasa a gaba illa bin hanyoyi da matakai da tage gani zata tsira iadan aka gudanar da wan nan zaben.

A misali a yanzu haka gwamnatin kasar ta iraqi tace a kwai alamun cewa wan nan zabe za a iya gudanar dashi a tsawon mako biyu ko kuma uku sabanin tunanin mutanen kasar na ayi a rana daya a kare a wan nan ranar.

Aiwatar da wan nan mataki dai a cewar gwamnatin kasar ka iya taimakawa wajen bawa dukkannin yan kasar gudanar da yancin su na yan kasa a hannu daya kuma da inganta harkokin tsaro a kasar.

A cewar shugaban hukumar zaben kasar Hussein Hendewi,ya shaidar da cewa matukar gwamnati ta gabatar musu da wan nan mataki a hukumance to babu shakka zasuyi nazarin sa tare da duba yiwuwar aiwatar dashi idan hakan zai dace da yanayin yan kasar.

A waje daya kuma da yawa daga cikin shugabannin yan darikar sunni na ganin cewa akwai sake game da wan nan zabe domin kuwa rashin kyakkyawan tsaro a yankunan su ba zai basu su gudanar da kamfe ba yadda ya kamata.

Shi kuwa wakilin mdd a kasar ta Iraqi Lakhdar Brahimi cewa yayi da wuya a gudanar da zaben adalci da gaskiya a kasar iraqi a halin da kasar take ciki yanzu na rashin tsaro. A don haka kamata yayi a dage wan nan zabe izuwa wani lokaci a nan gaba.

Haka shima shugaban kasar Russia Vladimir Putin ya fadawa faraministan na Iraqi Iyad Alawi cewa yaya yan kasar ta iraqi zasu gudanar da wan nan zabe bisa yanci da walwala bayan ga dakarun mamaye fal a cikin kasar tasu.

Shugaban dai na Russia ya fadi hakan ne a lokacin ganawar su da Faraministan a can birnin Mosco lokacin da Iyad Alawin ya kai wata ziyara a kasar.

Ibrahim Sani.