Matasa na fuskantar matsar rashin aiki a Ghana
July 6, 2018Sekondi-Takoradi tagwayen birane ne a kasar Ghana. A gefe guda ruwan kogi ne ke ratsa gine wasu ginen zamani da kuma tsoffin gidaje, can kuma ga jiragen ruwa mallakin kamfanonin mai na shawagi a kan ruwan.Wannan birni dai na cike da tarin arziki, sai dai kawo yanzu 'yan yankin ba su gani a kasa. To my right, wani tudun shakatawa ne da matasa marasa ayyukan yi ke haduwa a kusa da bakin ruwa.Edward Danda Swigam na cikin matasan da ke ganin basa cin wata riba daga masanantun mai da ke yankin. Da irin wannan kosa kosai koyon sanaoin, matasan na fatan kwace damar su ta ayyuka da 'yan ci rani suka mamaye a kamfanonin da ke yankin su. 'Yan ci rani ne da suka iya aiki ne ke samun aiki, amma cibiyar bunakasa ci gaban yammacin kasar ta bullo da tsarin ba wa matasan horo na musamman domin rage zaman kashe wando.