1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lebanon: Hariri zai kafa sabuwar gwamnati

Abdul-raheem Hassan
October 22, 2020

Shugaban kasar Lebanon Michel Aoun ya tabbatar da tsohon firaiministan kasar Saad Hariri a matsayin wanda zai jagoranci kafa sabuwar gwamnati a kasar domin ceto Lebanon daga matsayin tattalin arziki a cikin gaggawa.

https://p.dw.com/p/3kHVU
Den Haag UN-Sondertribunal zum Libanon Prozess Hariri Mord Saad Hariri
Hoto: picture-alliance/AP Photo/L. van Putten

Sabon Firaimionitan ya samu gagarumin rinjaye a majalisa da kuri'u 65, wannan shi ne karo na hudu Haririn ke zama Firaiministan Lebanon bayan da ya yi murabus a bara sakamakon jerin zanga-zangar kin jinin gwamnati saboda tsadar rayuwa da zargin cin hanci.

Sabon Firaiministan Saad Hariri ya yi alkawarin aikin ba tare da nuna banbancin siyasa ko ra'ayi ba, ya ce wannan dama ce ta sake gina tattalin arzikin kasar Lebanon da ke fuskantar barazanar durkushewa.