1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kwango: An halaka jakadan kasar Italiya

Ramatu Garba Baba
February 22, 2021

Jakadan Italiya na daga cikin mutane ukun da suka mutu a wani harin kwanton bauna a yankin Goma na Jamhuriyyar Dimokradiyyar Kwango.

https://p.dw.com/p/3pi4b
Italienischen Botschafters im Kongo, Luca Attanasio
Marigayi Luca Attanasio jakadan Italiya a KwangoHoto: AFP/Italy's Foreign Ministry

Hukumomin Kwango sun tabbatar da mutuwar jakadan kasar Italiya da wasu mutum biyu a sakamakon wani hari da ake zargin na kwanton bauna ne, da aka kai kan wani ayarin motocin jami'an Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya a yankin wato World Food Programme (WFP) a Goma na jamhuriyyar ta Kwango mai fama da rikici. Gwamnatin Italiyan, ta tabbatar da labarin mutuwar jakadan  mai suna Luca Attanasio, sanarwar ta ce ya mutu ne a wani asibiti da ke birnin Kinshasa a sakamakon raunin da ya ji daga harin.


Attanasio, yana da shekaru 43 a duniya, ya kuma soma aikin jakadancin ne tun daga shekarar 2017, baya ga Kwango yayi aiki a Moroko da Najeriya a matsayin jakadan Italiyan. Shugaban kasar Italiya Sergio Mattarella, yayi alla-wadai da harin da ya kira irin na ragwaye. A nata bangaren, rundunar sojin Kwango ta ce ta kaddamar da samame don gano wadanda suka kai harin na wannan Litinin.