Harin ′yan bindiga a Amirka | Labarai | DW | 13.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin 'yan bindiga a Amirka

Jami'an 'yan sanda na ci gaba da zaman ko ta kwana a birnin Dallas na Amirka bayan da wasu 'yan bindiga suka bude wuta a ofishinsu da ke birnin.

Hari a ofishin 'yan sanda a Amirka

Hari a ofishin 'yan sanda a Amirka

Rahotanni sun nunar da cewa ana kyautata zaton jami'an 'yan sanda sun samu nasarar cafke wani ko kuma wasu daga cikin 'yan bindigar. An dai samu abubuwa masu fashewa a harabar shalkwatar 'yan sandan na Dallas. Shugaban rundunar 'yan sandan birnin na Dallas David Brown ya shaidawa manema labarai cewa shaidun gani da ido sun tabbatar da ganin wata moto dauke da makamai da sanyin safiya ta dunfari ofishin 'yan sandan tare da bude wuta a kan mai uwa da wabi da kuma jefa abubuwa masu fashewa. Brown ya kara da cewa 'yan sanda sun samu nasarar yiwa motar kawanya inda suka cafke guda daga cikin maharan.