Harin ta'addanci ya kashe sojojin Mali biyar
June 17, 2017Talla
Wani dan majalisar yankin wanda bai so a ambaci sunansa ba, ya kwarmata wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, an kai harin ne da karfe biyar na asubahin wannan Asabar, kuma maharan sun lalata illahirin kayan aikin sojojin gwamnatin da ke a cikin wannan barikin soja da ke a nisan kilomita 80 da birnin Tombouctou daya daga cikin manyan biranen yankin Arewacin kasar.
Wasu shaidun gani da ido a garin na Bintagoungou sun ce maharan sun kwashi ganimar kayan yaki mai yawa kana sun kama wasu sojojin sun tafi da su. Wata majiyar sojojin Malin ta tabbatar da afkuwar lamarin ba tare da bayar da wani cikakken bayani ba.