Harin ta′addanci a kan sojoji a Mali | Labarai | DW | 14.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin ta'addanci a kan sojoji a Mali

Harin ƙunar baƙin wake ya hallaka dakarun kiyaye zaman lafiya biyu na Majalisar Ɗinkin Duniya guda biyu a kasar Mali.

Wani harin ƙunar baƙin wake ya hallaka dakarun kiyaye zaman lafiya biyu cikin yankin arewacin ƙasar Mali. Wata majiyar Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce lamarin ya faru a garin Kidal, kwana guda kafin gudanar da zaɓen 'yan majalisa zagaye na biyu, kuma zaɓen na zama matakin ƙarshe na tabbatar da komawar ƙasar bisa tafarkin demokraɗiyya bayan juyin mulkin da sojoji suka yi. Akwai wasu dakarun da suka samu raunika sakamakon harin kan dakarun kasashen Afirka.

Dakarun na aikin tabbatar da zaman lafiya bayan fattakar mayaƙan 'yan aware da masu kaifin kishin Islama da suka mamaye yankin na arewacin ƙasar ta Mali.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Abdourahamane Hassane