Harin ta′addanci a Indonesiya | Labarai | DW | 14.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin ta'addanci a Indonesiya

Wasu 'yan kunar bakin wake sun kai wasu munanan hare-here akan wata cibiyar hadahadar kasuwanci da ke a Jakarta Babban birnin kasar inda ya hallaka mutane da jikkata wasu

A kalla dai an sami tashin fashewar wasu boma-bamai uku a birnin na Jakarta, a inda aka shafe sa'o'i ana bata kashi tsakanin maharan da jami'an tsaron kasar.

A yayin da yake jajantawa al'ummar kasar shugaban kasar Indonesiya Joko Widodo ya yi nuni da cewar.

"Mun yi Allah wadai da wadan nan hare-haren da suka kawo barazanar lafiyar al'umma, tuni na baiwa hukumomi umarnin kamo wandan da suke da alhakin kai hare-haren. A matsayin mu na 'yan kasa bai kamata mu razana ba, ya kamata mu zauna cikin nutsuwa domin kamai zai dawo dai-dai".

Wata majiya ta bayyana cewar mayakan kungiyar IS ne suka kai harin. Inda mutane biyu suka mutu wasu mutake akalla goma suka jikkata