Harin kunar bakin wake ya hallaka mutane bakwai a Mali | Labarai | DW | 27.02.2013
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Harin kunar bakin wake ya hallaka mutane bakwai a Mali

Wani harin kunar bakin wake da mota dauke da bam, ya hallaka mutane bakwai a garin Kidal.

Wani harin kunar bakin wake da mota dauke da bam, ya hallaka mutane bakwai, a garin Kidal na arewacin kasar Mali.

Kungiyar 'yan awaren Azbinawa ta ce harin na yammacin wannan Talata da ta gabata, kusa da wajen duba ababen hawa, ya yi saniyar hallaka 'yan kungiyar bakwai, yayin da wasu su ka samu raunuka.

A cikin makon da ya gabata an samu makamancin wannan hari na kunar bakin wake da ya hallaka mutane biyu. Wata kungiya mai nasaba da al-Qaeda ta dauki alhakin kai hare haren.

Dakarun sojan Faransa da Chadi na ci gaba da aikin tabbatar da kawo karshen mayaka cikin garin na Kidal da ke yankin arewacin kasar ta Mali.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu

 • Kwanan wata 27.02.2013
 • Muhimman kalmomi Mali
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/17mNE
 • Kwanan wata 27.02.2013
 • Muhimman kalmomi Mali
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/17mNE